Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Dan majalissa ya nemi a binciki yanda ake kashe kudaden tsaro a jihar Katsina
Dan majalissa ya nemi a binciki yanda ake kashe kudaden tsaro a jihar Katsina

Dan majalissa ya nemi a binciki yanda ake kashe kudaden tsaro a jihar Katsina

0

Dan Majalissa Mai wakiltar Karamar Hukumar Mani, Rt. Hon. Aliyu Sabiu Muduru a wani zama da akayi a majallisa yayi kira ga Majalissar dokoki da ta aiwatar da bincike akan yanda ake kashe kudaden tsaro a jihar Katsina.

Kiran ya biyo bayan yawaitar samun karuwar hare-haren yan bindiga daya jaza tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar nan.

A cikin wani faifan bidiyo dake yawo a kafar sadarwar zamani, tsohon kakakin majalissar yayi kira ga majalissar data bincika kuma ta tabbatar da yanda ake kashe kudaden harkar tsaro a Jihar.

A cewar shi, Binciken Majalissar zai fidda tantama tare da tabbatar da hakikanin gaskiyar lamarin ko Gwamnatin jiha na ba jami’an tsaro tallafin daya kamata domin tunkarar matsalar tsaro a jihar ko a’a.

Dan Majalissar ya kara da cewa tsarin dokoki ya bada dama ga majalissar tayi bincike game da yanda ake kashe kudaden gudanar da harkar tsaro a jihar.

A cewarshi “A cikin masu ruwa da tsaki a harkar tsaro akwai mai taimakama Gwamna akan tsaro, akwai ofishin Gwamna, ofishin sakataren Gwamnati wanda tananne ake tafiyar da kudaden gudanar da harkar tsaro”.

Ya cigaba da cewa“Saboda haka ni ina bada shawara a tsaya a kalli abin nan sosai.  Kwamitin tsaro a Majalissar ya kamata ya kawo ma majalissar bayani na abinda ya faru dangane da tsaro daga Juniaru zuwa watan Augusta”.

“Idan har yan kwamitin sun sani tilas su hanzarta yima majalissar bayani idan kuma basu sani ba toh su fadi ya akayi basu sani ba ko an sanar dasu basu sanarda majalissa ba?”.

Katsina Post idan baku manta ba ta ruwaito cewa a ranar litinan data gabata ansha kokekoke a majalissar dokokin jihar Katsina saboda gazawar gwamnati waje samar da tsaro.

Hakazalika mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari yayi kira ga al’umma dasu mallaki makamai domin su kare kansu daga hare-haren yanbindiga, lamarin daya yanyo cece-kuce a fadin kasar.

 

 

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: