Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Mutanen gari sun fara hada kudi suna siyen makamai a Katsina
Mutanen gari sun fara hada kudi suna siyen makamai a Katsina

Mutanen gari sun fara hada kudi suna siyen makamai a Katsina

0

Mutanen gari sun fara hada kudi suna siyen makamai a Katsina

Al’ummar garuruwa da dama musamman ma masu fama da matsalar tsaro sun soma yin karo-karo na kudi domin siyen makaman da za su kare kan su a jihar Katsina.

A wani rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ta bayyana cewa mutanen garuruwa irin su Batsari da Jibia tuni sun yi nisa cikin wannan tsarin.

Al’ummar dake garuruwan da ke fama da matsalar ta’addancin dai sun bayyana cewa tuni suka fahimci cewar tashi su kare kan su shine kadai mafita.

Sun bayyana cewa zaman jiran jami’an tsaro su kare su bai haifar masu da da mai ido ba.

Wani dan karamar hukumar Batsari da aka tattauna da shi ya bayyana cewa yanzu matsalar da suke fuskanta ita ce makaman da ke gare su ba su kai na filanin ba don a lokutta da dama ko jami’an tsaro ba su da irin makaman da filanin ke rikewa.

Haka ma dai wani dan garin Kurfi duk dai a jihar ta Katsina ya bayyana cewa su a bangaren su ma manyan garin ne suka hada kudi suka siyo masu makaman domin su kare kan su.

Ya kara daukaka ya cewa kuma lamarin haka yake are wasu garuruwan da dama domin kuwa suna musayar bayanai masu muhimmanci da su.

In dai ba’a manta ba Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a kwanan baya yayi kira da mutane su tashi su nemi makamai su kare kan su.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: