Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An Chafke Dan Achaba Yana Yunkurin Satar Mutum 2 A Katsina 
An Chafke Dan Achaba Yana Yunkurin Satar Mutum 2 A Katsina 

An Chafke Dan Achaba Yana Yunkurin Satar Mutum 2 A Katsina 

0

An Chafke Dan Achaba Yana Yunkurin Satar Mutum 2 A Katsina 

Rundunar Jami’an Tsaron Lafiyar Yan Kasa ta Jihar Katsina, ta samu nasarar kame wani dan achaba da yayi Yunkurin satar wasu Dalibai su biyu na Makarantar Family Support dake cikin Birnin katsina.

Kakakin Rundunar DSC Muhammad Abdara ne ya gabatarda Wanda ake zargin a Shelkwatar Hukumar dake Katsina.

Kamar yadda DSC Abdara ya bayyana an chafke wanda ake zargin ne a dai-dai lokacinda yayi yunkurin satar yara biyu yan makarantar ta Family Support.

Yace Jami’an Hukumar da aka ajiye aiki kusa da makarantar ne suka chafke mutumen bayanda mahaifinsu ya sanar da su akan faruwar lamarin.

Wanda ake zargin dai mazaunin Kauyen Unwalar Jangefe ne dake a cikin Karamar Hukumar Batagarawa.

DSC Abdara ya hori Hukumomin Makarantu da iyaye akan su kara zama masu taka tsantsan wurin kula da masu daukar yaransu a lokacinda aka tashi makaranta.

Ya kuma nanata kudirin Hukumar ya NSCDC a Jihar Katsina na cigaba da yin bakin kokarinta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Daga nan sai yace Sashen Bincike na Rundunar ya tsunduma wurin gano wadanda ake zargin cewa sunzo satar yaran tare da wanda aka chafke din.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: