Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA ‘Yan bindiga sun shiga makarantar Islamiyya, sun sace dalibai a Katsina
‘Yan bindiga sun shiga makarantar Islamiyya, sun sace dalibai a Katsina

‘Yan bindiga sun shiga makarantar Islamiyya, sun sace dalibai a Katsina

0

‘Yan bindiga sun shiga makarantar Islamiyya, sun sace dalibai da malamin su a Katsina 

Yan bindiga sun sace dalibai da dama da malami guda daya a makarantar Islamiyya da ke kauyen Sakkai a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

A cewar rahoton na Daily Trust, an sace daliban ne yayin da suke daukar darrusa a harabar makarantar da yamma.

Kazalika, an kashe mutane uku a yayin da yan bindiga suka kai hari a garin Batsari, hedkwatar karamar hukumar Batsari na jihar Katsina.

Wani mazaunin Batsari ya shaidawa majiyar mu cewa daya daga cikin wadanda abin ya shafa wacce gwagwon sa ce ta rasu sakamakon buguwar zuciya saboda tsoron harbin bindigan yan fashin dajin.

Ya kuma ce sauran mutane biyun sun mutu ne sakamakon harsashi da ya ratsa jikinsu.

Ya ce: “A lokacin da yan bindigan suka taho Batsari, mun gano cewa jami’an tsaro suna can kauyen Dankar inda yan bindigan suka musu kawanya.”

Ya kara da cewa an sace mutum takwas yayin harin na Batsari.

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya ce zai tuntubi DPO na Batsari domin sannin tabbas kafin ya yi tsokaci a kan harin na Faskari domin sojoji ke kula da garin.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: