Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gwamna Masari ya umurci mutane su dauki makamai su kare kan su
Gwamna Masari ya umurci mutane su dauki makamai su kare kan su

Gwamna Masari ya umurci mutane su dauki makamai su kare kan su

2

Ku ɗauki makamai don kare kanku daga ‘yan fashi – Gwamnan Katsina Aminu Masari 

Gwamna Masari ya umurci mutane su dauki makamai su kare kan su

Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ya buƙaci mazauna garuruwan da ‘yan bindiga ke yawan kai wa hare-hare da su nemi makamai don kare kan su daga hare-haren.

Aminu Bello Masari ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da ya kai ziyarar jaje a Ƙaramar Hukumar Jibia ga iyalan mutum 10 da jami’an hukumar kwastan suka kashe a makon da ya gabata.

Katsina na cikin jihohin da ‘yan bindiga suka fi kashewa tare da yin garkuwa da mutane a arewa maso yamnmacin Najeriya.

Ranar 11 ga watan Disamba ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka sace ɗalibai daga sakandaren garin Kankara na jihar ta Katsina guda 344, inda suka shafe kwana shida a hannun masu garkuwar.

“Miƙa wuya da mutane ke yi ga ‘yan fashi shi ke jawo ɓarayin su ci gaba da aikata munanan lamura a lokuta da yawa,” a cewar Masari cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Abdu Labaran Malumfashi ya fitar.

Ya ƙara da cewa “wajibi ne mutane su daina tunanin cewa harkar tsaro ta gwamnati ce ita kaɗai”.

Kazalika, gwamnan ya umarci mutanen yankin da kar su yarda da duk wani ihsani da hukumar kwastan za ta yi musu “har sai an nema wa iyalan waɗanda aka kashe haƙƙinsu”.

Comment(2)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: