Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Tawagar jaje ta kwastam ta gamu da fushin masu ruwa da tsaki a Katsina

Tawagar jaje ta kwastam ta gamu da fushin masu ruwa da tsaki a Katsina

0

Gwamnatin Jihar Katsina za ta shigar da hukumar Ƙwastam ta ƙasa ƙara…Masari

Tawagar jajantawa ta kwastam ta gamu da fushin masu ruwa da tsaki a Katsina 

Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina za ta shigar da hukumar ƙwastam ta ƙasa ƙara, ma damar bata biya diyyar rayukan da jami’an ta sukai sanadiyyar salwantar su ba a garin Jibia, tare kuma da hukunta jami’an da sukayi wannan ganganci da ya haddasa wannan asarar rayuka da jikkata wasu bayin Allah.

Zuma Times Hausa ta jiyo ta bakin mai Taimakawa Gwamnan Jihar Katsina akan kafafen sadarwar zamani Abdulhadi Ahmad Bawa yana cewa, Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a yayin da ya amshi tawagar da Shugaban Hukumar ya turo domin jajanta wa al’umma da Gwamnatin Jiha kan wannan mummunan al’amari da ya faru ranar 9 ga watan nan a garin Jibia.

Alhaji Aminu Bello Masari wanda bacin ranshi ya fito fili, ya nuna takaici kan yadda jami’an hukumar suke bin wanda ya dauko shinkafa buhu biyar a kan mashin kamar wanda yayi kisan kai, alhali kuma ga ‘yan ta’adda suna gallaza wa al’umma amma sun kasa yi masu komai. Haka kuma, yasa babbar alamar tambaya a kan yadda jami’an hukumar suke da wuraren binciken motoci (check point) har guda ashirin da takwas (28) a kan hanyar da bata fi kilomita arba’in (40) ba. Tare da bayyana cewa, hakan, na cikin abinda ya tilastawa mutane da yawa bin barauniyar hanya.

Haka zalika Zuma Times ta ji cewa Gwamnan ya kuma ja hankalin hukumar da ta sauya salon yadda take hulda da kuma daukar al’ummomin dake kan iyakokin ƙasar nan, musamman masu iyaka da Jamhuriyyar Nijar. Domin a yanzu suna ɗaukar su kamar ba ‘yan Najeriya ba, sun saka su cikin takura, tsangwama da kunci duk da sunan hana fasa ƙwabri da kuma tara kuɗin shiga.

Ya kara da cewa, ko alama, Gwamnatin Jiha ba ta goyon fasa ƙwabri ko wane iri kuma ko ta wace hanya, amma tana da wajibcin tabbatar da walawalar al’umma da tsaron rayukan su da dukiyoyin su. A saboda haka, ya gargadi hukumar da ta tabbatar da cewa wannan shi ne Karon ƙarshe da irin hakan za ta faru.

Tun farko a nashi jawabin, jagoran tawagar, ACG Uba Garba Mohammed ya bayyana cewa Shugaban Hukumar na ƙasa ya turo su wakilce domin isar da ta’aziyya gami da jaje ga al’umma da kuma gwamnatin jihar kan mummunan hadarin da ya faru a cikin garin jibiya wanda kuma har yayi sanadiyyar rasa rayuka da kuma jikkata wasu bayin Allah.

Ya ƙara da cewa Shugaban nasu ya umurci su tattauna da iyalan wadanda suka rasun, al’umma da kuma shuwagabannin su domin samo hanya mafi dacewa ta warware wannan matsala.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: