Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Ƴan Bindiga Sun kone Kauyuka a Katsina, Sun Kashe Mutum 5 A Wasu Sabbin Hare-Hare
Ƴan Bindiga Sun kone Kauyuka a Katsina, Sun Kashe Mutum 5 A Wasu Sabbin Hare-Hare

Ƴan Bindiga Sun kone Kauyuka a Katsina, Sun Kashe Mutum 5 A Wasu Sabbin Hare-Hare

1

Ƴan Bindiga Sun kone Kauyuka a Katsina, Sun Kashe Mutum 5 A Wasu Sabbin Hare-Hare 

Kashe Mutum Biyar Da Kone Wasu Kone Wasu Gidaje A Kananan Hukumomin Musawa Da Matazu A Jihar Katsina

Yan bindiga dauke da bindigogi sun kai hari a wasu Kauyukan Kananan Hukumomin Musawa da Matazu inda suka kashe mutum biyar har lahira da sace dabbobi da dama da kuma kone wasu Kauyukan daga Alhamis zuwa daren jiya Asabar.

Majiyar Katsina Post dake yankin ta shaida mata cewa yan bindigar sun kai harin a cikin karamar hukumar Musawa, a daren Juma’a inda suka kore dabbobi da dama, sun shiga garin da misalin karfe takwas da hamsin, sun kwashe tsawon awa guda cikinsa, amma ba su kashe kowa ba, sun dai saci dabbobi.

A daren Asabar, yan bindigar sun kai hari a kauyen Dugul dake gundumar Mazoji Yalwa Papu a karamar hukumar Matazu, inda suka kashe mutum huɗu, ciki har da Mai Unguwar garin, Malam Rabi’u. Sun kone gidaje da dama na garin tare da kwashe masu

Majiyar ta ci gaba da cewa sun kai makamanci harin a wani kauyen Gidan Mamman Dangata dake arewacin Musawa, suka yi musayar wuta tsakanin mutanen gari da yan bindigar, inda suka kashe mutum daya cikin yan gari da raunata mutum daya, su ma yan garin sun kashe dan bindiga guda har lahira, amma yan bindigar sun samu nasarar kore masu shanu masu shanu.

Majiyar Blueink News Hausa ta nakalto cewa daren jiya Asabar, yan bindigar sun kai hari a kauyen Ilali, dake cikin karamar hukumar Matazu, inda suka dira gidan wani mutum, Allah ya sa ya boye kan rufin gidansa da ya ji tahowarsu, sai suka rufe dakinsa suka banka wa dakin wuta, sanadiyyar hakan ya kone a wasu sassan jikinsa, yanzu haka yana kwance a babbar Asibitin garin Malumfashi yana jinyar konewar da ya samu.

Haka zalika, sun kashe mutum daya, tare da kone gidaje da dama, da kuma balle shagunan yan kasuwar garin da sace dabbobi masu dinbin yawa.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: