Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Mustapha Inuwa ya aurar da dan sa na farko a wani daurin aure na ‘ba zata’
Mustapha Inuwa ya aurar da dan sa na farko a wani daurin aure na ‘ba zata’

Mustapha Inuwa ya aurar da dan sa na farko a wani daurin aure na ‘ba zata’

0

Mustapha Inuwa ya aurar da dan sa na farko a wani daurin aure na ba-zata 

A yau, Asabar, 14/8/2021 ne aka daura auren Muhsin Mustapha Muhammad Inuwa da amaryarsa Rahama (Dhalila) Buhari Bala a Birnin Kebbi, jihar Kebbi.

Gwamnan Jihar Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari ya amshi auren a matsayin shi na wakilin ango, a yayin da Gwamnan Jihar Kebbi, Sen. Abubakar Atiku Bagudu ya bada Rahama a matsayin shi na waliyyin amarya.

A cikin hudubar daurin auren, Gwamna Abubakar Bagudu ya ce ya aurar da Rahama ga Muhusin akan sadaki Naira Dubu Dari wanda Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ya biya lakadan, yayin da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya bada kudin malamai.

Daurin auren wanda aka yi fadar Wakilin Sarkin Gwandu, ya samu halartar.

Iyaye da aminan Uban Ango (SGS, Mustapha Inuwa) wadanda suka rufa ma Wakilin Ango, Gwamna Aminu Bello Masari baya.

Sun kuwa hada da Shugaban rukunin kamfanonin Afdin da Jiragen Saman MaxAir, Alhaji Dahiru Barau Mangal da Babban Jojin Jihar Katsina, Maishari’a Musa Danladi Abubakar da Kwamishinan Shari’a, Ahmed Elmarzuq da Kwaminan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Alhaji Faruk Jobe da Shugaban Jamiyyar APC na Jihar Katsina, Malam Shitu S. Shitu da Shugaban Asusun Tallafin Karatu, Alhaji Isa Ame da Sheikh Hadi Balarabe da dai sauran su.

Tuni tawagar Wakilin Ango, Gwamna Aminu Bello Masari ta safka gida lafiya.

Tawagar ‘yan daurin auren wadda ta safka a filin jirgin saman Umaru Musa Yar’adua dake nan Katsina ta samu kyakkyawar tarba daga Uban Ango, Mustapha Muhammad Inuwa tare da ‘yanuwa da abokan arziki da kuma wasu jami’an Gwamnati.

Sakataren Gwamnatin wanda ya ke cike da farin ciki, ya yi hamdala ga Allah SWT da ya nuna masa wannan rana tare da mika godiya ta musamman ga Gwamna Aminu Masari da Alhaji Dahiru Mangal da Babban Jojin da Shugaban Jamiyyar APC na jiha da daukacin ‘yantawagar da sauran jama’a da suke yi masu fatan alheri.

Abdullahi Aliyu Yar’adua

Director Press

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: