Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An gina masana’antar kilishi ta zamani mai anfani da hasken rana a Katsina
An gina masana’antar kilishi ta zamani mai anfani da hasken rana a Katsina

An gina masana’antar kilishi ta zamani mai anfani da hasken rana a Katsina

1

Jihar Katsina ta samu Masana’antar Sarrafa Kilishi Mai Amfani da Haske Rana…

An gina masana’antar kilishi ta zamani mai anfani da hasken rana a Katsina 

Kaɗan daga cikin ribar da jihar Katsina ta samu daga Hukumar nan mai kula tareda Magance zaizayar ƙasa da Inganta Madatsun Ruwa ta Ƙasa ƙarƙashin kulawar Babban Bankin Duniya wato Newmap, shine samuwar Masana’antar da ale Sarrafa Kilishi ta hanyar amfani da hasken Rana.

Ita dai wannan Hukumar bayan kula da Inganta Madatsun Ruwa ta zarce kuma wajen nemawa Al-umma hanyoyin sauƙaƙa rayuwar Yau da kullum tareda habɓaka tattalin Arzikin su, Hukumar ta ware kuɗi kimanin Naira Milyan Sittin da Biyar wajen ganin wannan katafariyar Masana’antar mai ɗauke da wurin Sarrafa Kilishi na zamani da ya haɗa da Ɗakin Sarrafa Kilishin da Rijiya mai samar da Ruwa da ma Hitulun kan hanya.

Mazauna yankin Marabar Ƙanƙara ta jihar Katsina sune suka ci gajiyar wannan shirin Inda kuma suka nuna jin daɗin su akan hakan, sun bayyana cewa a Baya zai ɗauki Mutum ƙwanaki Ukku zuwa Hudu kafin ya haɗa Kilishi tundaga yankan Dabba zuwa gyaranta da shanyarta a Rana ta bushe kafin nan a gyarata zuwa Kilishi, yanzu kam cikin abunda bai haura Awwanni Ukku ba sai a haɗa Kilishi kuma a saida shi.

Wannan Masana’antar zata iya Sarrafa Naman Sanuwa Takwas a Rana Guda, wanda hakan yake nuna cewa za’a samu ƙaruwar ayyukan yi, kuma wannan tsarin yafi tsabta babu kuda bare ƙura.

Comment(1)

  1. Wannan abun ya Nigeria Yakamata kuma ku nema wa kilshin kasuwa domin ya samu karɓuwa sannan yana dakyau a inganta shi ga dukkanin jahohin arewa maso yamma.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: