Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An yi kuskuren binne wata yarinya da ran ta a Katsina
An yi kuskuren binne wata yarinya da ran ta a Katsina

An yi kuskuren binne wata yarinya da ran ta a Katsina

1

An yi kuskuren binne wata yarinya da ran ta a Katsina

Wani abun al’ajabi da mamaki ya faru a garin Kafur cikin karamar hukumar Kafur din jihar Katsina inda muka samu labarin cewa an yi kuskuren binne wata yarinya da ran ta.

Kamar yadda muka samu labari, yarinyar mai suna Sa’adatu Hassan Kafur dai ta yi doguwar suma ne sakamakon wutar lantarkin da ta taba jiya da marece wanda har aka yi tunanin ta rasu.

Wani dan garin wanda ya bukaci mu sakaya sunan sa ya shaida mana cewa bayan doguwar suman da yarinyar tayi iyayen ta sun kai ta wata asibiti mai zaman kan ta a garin Kafur din inda ma’aikacin lafiyar da aka tadda ya fada masu cewar ta rasu.

“Da abun ya faru Iyayen ta sun kai ta wata asibi nan garin amma likitan sai ya ce ta rasu. Daga nan ne ma suka maido ta gida aka yi mata wanka aka yi mata sutura. Amma da yake dare yayi, an iyalan na ta suka sanya jana’izarta idan gari ya waye.”

Majiyar ta mu ta kara da cewa da safiya ta yi kuma jama’a suka taru aka yi mata Sallah aka kuma kai ta makabarta aka binne ta kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Yadda Aka Gano Bata Mutu Ba

Majiyar mu ta kara da cewa bayan an binne yarinyar wadda ke aji biyar (5) a makarantar gaba da Sakandare, sai labari ya rika yawo a cikin gari da kuma tsakanin makusantan ta na shakku da kuma tababar mutuwar ta ta.

Wasu daga cikin mutanen da suka dauki gawar a makara ne suka fara bayyana cewa sun ji kamar cikin yarinyar yayi kuka kuma ta yi tusa, amma dai gudun jawo rudani da cece kuce, sai suka yi shiru.

Haka zalika ma cikin ‘yan uwan yarinyar da suka kwana da ita sun bayyana cewa sun ji motsi a cikin makarar amma sai suka yi tunanin ko bera ne a cikin dakin.

Daga karshe dai aka dunguma zuwa makabartar aka tone ramin sannan kuma aka fiddo ta da ran ta.

Ya Ya Ake Ciki Yanzu?

Da aka fiddo yarinyar da ran ta, iyalan ta sun dunguma zuwa asibin garin Malumfashi domin ceto rayuwar ta.

Saint dai labarin da muke samu yanzu shine bayan kokarin da aka yi na ceto yarinyar, ta rasu kuma har ma an yi jana’izar ta.

Comment(1)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: