Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Zan inganta tsaro tare da daukar ma’aikata idan na zama Gwamnan Katsina- Inji Jikan Hambali
Zan inganta tsaro tare da daukar ma’aikata idan na zama Gwamnan Katsina- Inji Jikan Hambali

Zan inganta tsaro tare da daukar ma’aikata idan na zama Gwamnan Katsina- Inji Jikan Hambali

0

Daukar Ma’aikata A Matakin Jiha Da Kananan Hukumomi Da Inganta Tsaro Zasu Samu Tagomashinda Ya Dace A Gwamnati Na – Jikan Hambali.

Dan Takarar Kujerar Gwamnan Jihar Katsina a Jam’iyar APC a Shekarar 20I9 Alhaji Garba Dankani, ya tabbatar da cewar idan al’umar Jihar Katsina suka zabeshi a matsayin Gwamnan jihar zai bayar da fifikonda ya dace ga batun daukar ma’aiktatah a matakin Jiha da Kananan Hukumomi gami da inganta harkokin tsaro.

Alhaji Garba Dankani wanda shine Shugaban Hukumar Gudanarwa Na Asibitin Kwararru Ta Kula Kunnuwa Ta Kasa dake Kaduna ya bayyana hakan ne a sa’ilinda yake zantawa da manema labarai akan kudurorinda zai sanya a gaba idan ya samu shugabancin Jihar Katsina.

Alhaji Garba Dankani wanda ya nuna damuwa akan yawaitar rashin ayyukanyi a tsakanin matasa da suka kammala manyan makarantu yace in Allah SWT ya bashi dama zaiyi aiki tukuru wurin shawo kan matsalar.

Akan abinda ya shafi tsaro kuwa Jikan Hambali ya tausayawa wadanda lamarin ya shafa,sai yace idan ya samu dama zaiyi bakin kokarinshi na ganin ya maido da martabar Jihar Katsina wurin zaman lafiya da lumana.

Ya kara da cewar sauran bangarorinda zasu samu tagomashinda ya dace sun hada da:

*Bayar da horon sana’oi ga matasa da mata
*Samar da ilimi kyauta a matakin Firamare da Sakandire
*Bunkasa kiwon lafiya
*Inganta noma da kiwo
*Bunkasa samar da ruwan sha a Birni da Karkara
*Inganta hanyoyin sufuri
*Kyautata jin dadin ma’aikatan gwamnati
*Samar da jin dadi ga masu bukata ta musamman da sauran masu karamin karfi.

Alhaji Garba Dankani yace wadannan da ma wasu bangarori zasu samu kulawa ta musamman daga wurin shi idan ya zama Gwamnan Jihar Katsina idan Allah yaso.

Daga nan sai ya bukaci al’umma akan kada suyi kasa a gwuiwa wurin jajircewa ta fuskar zaben mutane na gari da zasu shugabancesu wanda hakan shine matakinda zai kawo cigaban Jihar nan da kasa baki daya.

Jikan Hambali ya kuma kara jan hankalin magoya bayanshi akan kada su gajiya wurin wayar da kan al’umma akan kyawawan manufofinshi ga jama’ar Jihar Katsina.

Alhaji Garba Dankani ya nanata kudirinshi na cigaba da kasancewa mai biyayya ga Jam’iyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari.

Daga karshe yayi addu’a akan Allah SWT yayi jagoranci ga Shugaba Muhammadu Buhari da sauran shuwagabanni a dukkan matakai wurin sauke nauyinda aka dora masu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: