Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Tarihin Sarkin Katsina Sanau da Kokowar Sa da Sarki Korau A Shekarar 1348
Tarihin Sarkin Katsina Sanau da Kokowar Sa da Sarki Korau A Shekarar 1348

Tarihin Sarkin Katsina Sanau da Kokowar Sa da Sarki Korau A Shekarar 1348

0

Tarihin Sarkin Katsina Sanau da Kokowar Sa da Sarki Korau A Shekarar 1348 

Sarki Sanau, shi ne sarki Jibda Yaƙi. Sarki ne da ya fito daga zuriyar Durɓawa, haɓe ne shima.

Shi ne sarki na shida kuma na ƙarshe daga zuriyar Durɓawa kuma Haɓawa.

Mulkinsa ya zo ƙarshe a shekarar 1348 bayan buga shi da ƙasa da sarki Muhammadu Korau ya yi a kokwar da suka buga.

Kokowar Sarki Sanau Da Korau

Akwai ruwayoyi guda biyu dangane da wannan kokawa ta Sarki Sanau da kuma Sarki Korau.

Ta farkon wacce muka samu daga gidan mai garin Durɓi ta Kusheyi ta hanya isar da saƙon nan ta Kunne ya Girmi kaka, ta labarta mana cewa shi Korau lokacin da ya zo garin Katsina yana zaune sai ya riƙa yiwa matar sarki Sanau alheri, wato yana kyautata mata har sai da ya samu karɓuwa a wajenta ya kai matakin da duk abin da ya nema idan tana da shi za ta iya bashi.

Daga ƙarshe sai ya roƙe ta sanin sirrin ƙarfin kokawar sarki Sanau, sai ta sanar da shi cewa yana amfani da wata laya. Bayan wani ɗan lokaci sai ya sake roƙar ta cewa ta bashi wannan laya ta sarki Sanau yana da wata kokawa. Ta ɗan jinjina kafin ta bashi, amma dai daga ƙarshe ta bashi.

Da ya karɓi wannan laya sai ya kuma nemi Sarki Sanau da ya zo su buga kokawa, sarki sanau ya yi shela a gari ya kuma saka ranar kokawa, da rana ta zo Sanau ya waiwaici layarsa ya nema ya rasa, ya tambayi matarsa ta ce masa bata san ina ya ajiye ba.

Da aka buga kokawa sai Korau ya buga Sanau da ƙasa. Wannan kaye shi ya kawo ƙarshen sarautar Sanau kuma farkon Sarautar Korau.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: