Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA ‘Yan bindiga sun sako mutum 4 daga daji matsayin barka da Sallah a Katsina
‘Yan bindiga sun sako mutum 4 daga daji matsayin barka da Sallah a Katsina

‘Yan bindiga sun sako mutum 4 daga daji matsayin barka da Sallah a Katsina

0

‘Yan bindiga sun sako mutum 4 daga daji matsayin barka da Sallah a Katsina 

Daga misbahu batsari 

A ranar Juma’a 23-07-2021 aka sako wasu daga cikin wadanda ‘yan bindiga suka dauka a Batsari.

Idan ba’a manta ba, watanni biyu da doriya da suka gabata ‘yan bindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, suka dirar ma wasu unguwannin Batsari, inda suka kashe mutum daya, sannan suka sace mutane 28 da tarin dabbobi.

A jiya Juma’a Allah yayi fitowar wasu daga cikinsu.

Zantawar mu da mutanen da aka sako sun bayyana mana irin bakar azabar da suka sha ta yunwa da sauran kuncin rayuwa a zaman su dajin, inda har wani yaron goye ya rasa ransa.

An biya zunzurutun kudi kudi har naira miliyan biyu da rabi N2.5m da zimmar karbo matar Umar Tukur mai suna Hussaina da jinjirinta Al-ameen, sai suka karo masu da mutum hudu, sukace ga barka da sallah nan kamar yadda suka labarta mana.

Ga jerin sunayen mutanen da aka sako:

1. Hussaina Umar.

2. Al-ameen Umar.

3. Marwanatu Bello.

4. Zainab Bello.

5. Muhammad Bello.

6. Yakubu Bello.

Yanzu mutum ashirin da biyu ke hannun masu garkuwa da mutane.

Daga Katsina city news

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: