Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Tashar Gidan Talabijin Na Katsina KTTV, Ta Karrama Masu Kallon Shirin Duniya Labari
Tashar Gidan Talabijin Na Katsina KTTV, Ta Karrama Masu Kallon Shirin Duniya Labari

Tashar Gidan Talabijin Na Katsina KTTV, Ta Karrama Masu Kallon Shirin Duniya Labari

0

Tashar Gidan Talabijin Na Katsina KTTV, Ta Karrama Masu Kallon Shirin Duniya Labari.

Tashar Gidan Talabijin ta KTTV dake Katsina ta Karrama masu kallon sanannen shirinta na ‘Duniya Labari.

An gabatar da Lambar Yabon ne a lokacin wani taro da ya gudana a farfajiyar tasahar ta kttv.

Da yake jawabi a like kacin mika lambar yabon,Shugaban kamfanin Green House Katsina Alhaji Shehu Namaska wanda Manajan Kamfanin Alhaji Sani Shehu Namaska ya wakilta, yace kamfanin a shirye yake yaci gaba da hada hannu da tashar domin daukar nauyin shirin.

Alhaji Shehu Namaska ya yabawa tashar ta kttv akan shirye-shiryenta dake da manufar fadakarwa da ilimantar da al’umma akan batutuwa da suka shafesu.

A nashi jawabin,Jagoran shirin Malam Ahmed Mukhtar Yantaba ya yabawa Janar Manajan Tashar Alhaji Sani Garba Kuringafa da Kamfanin na Green House akan yadda suke dawainiya da shirin.

Ahmed Mukhtar Yantaba yace tashar ta kttv zata cigaba da bijiro da wasu sahihan hanyoyi na kara kwarin gwuiwa ga masu kallon shirin na Duniya Labari da ma masu kallon sauran shirye-shiryen tashar.

A madadin wadanda aka Karrama,Malam Aliyu Yansiliyu ya yabawa tashar ta kttv akan karamcin,sai ya nanata kudirinsu na cigaba da kasancewa da shirye-shiryen tashar.

Wadanda aka Karrama din sun hada da Yahayya Nuhu Tudun Yanlihidda da Sadiya Bala Kankia gami da Aliyu Yansiliyu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: