Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Durɓi ta Kusheyi: Tarihin Asalin Mazaunin Fadar Masarautar Katsina
Durɓi ta Kusheyi: Tarihin Asalin Mazaunin Fadar Masarautar Katsina

Durɓi ta Kusheyi: Tarihin Asalin Mazaunin Fadar Masarautar Katsina

1

Durɓi ta Kusheyi: Tarihin Asalin Mazaunin Fadar Masarautar Katsina

Durɓi gari ne a cikin jahar Katsina, wanda ke da tazarar kusan kilomita 32 daga birnin Katsina. Wannan gari shi ne asalin fadar masarautar Katsina. Akwai abubuwan tarihi a wannan gari da ke tabbatar da kasantuwarsa fadar mulkin Katsina ta farko.

Wannan gari yanzu an fi kiransa da Durɓi ta Kusheyi saboda samuwar kusheyi (ƙaburbura) irin na mutenen da. Wasu daga cikin ruwayoyin da muka samu na kunne ya girmi kaka sun labarta mana cewa kusheyin guda shida ne adadin sarakunan da suka zauna a garin kafin komawar garin Katsina. Amma a wani ƙauli sun ce ba wai kusheyin sarakuna ba ne, a’a, kusheyi ne dai na jama’ar gari saboda a al’adar mutanen gurin idan mutum ya mutu akan binne shi da dukkan abubuwan da ya mallaka.

Wannan ra’ayi ya samu goyon bayan hukumar tarihi da al’adu ta Katsina (History and Culture Bureau), wanda wani jami’inta ya gaya mana cewa akwai wasu abubuwa da masana tarihiri suka haƙo wanda ke tabbatar da faruwar wancan zance, ita ma dai wannan maganar bata samu ƙarfafa da gani na zahiri game da shi abin da aka tono ɗin ba.

Daga cikin abubuwan tarihin da har yanzu ke raye a wannan gari akwai fadar masarautar wacce ke kewaye da duwatsu da suke a jere kamar Katanga da kuma sarƙin bishiyoyi. A cikin fadar a kwai wata kuka mai suna ‘Katsi’, wacce wasu ke alaƙanta samuwar sunan Katsina daga ita wannan kukar.

Fadar Sarakunan Farko ta Katsina da ke garin Durbi ta Kusheyi
Kukar Katsi

Sannan kuma akwai wani dutse mai ban al’ajabi da ake kira ‘Dutsen Bataretare’, dutsen da aka ce shi sarki Batare da jama’arsa suka bautawa. Majiyar kunne ya girmi kaka ta labarta mana cewa a wancan zamanin ana yiwa wannan dutse yanka, saboda haka idan mutum ya taka shi to zai haukace ko kuma ya mutu.

Dutsen Bataretare

Sannan kuma akwai kusheyin mutanen da, wato ƙaburbura, waɗanda daga su ne aka canjawa garin suna ya zama Durɓi ta Kusheyi.

Wani ƙabarin Mutananen Dauri (Kushewa)

Sannan kuma dai shi garin ya sha zama kushewa a kankansa, sai kuma daga baya mutane su sake komawa su zauna a cikinsa. A yanzu haka nan akwai jama’a a wannan gari.

Comment(1)

  1. Assalamu alaikum.
    Dan Allah a wane karamar hukuma wannan garin yake?

    Har yanzu ana zuwa wadannan wuraren?

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: