Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Za’a maida gidajen kallo makarantun Islamiyya a Katsina
Za’a maida gidajen kallo makarantun Islamiyya a Katsina

Za’a maida gidajen kallo makarantun Islamiyya a Katsina

0

Majalisar Katsina za ta maida gidajen kallo makarantun Islamiyya

Za’a maida gidajen kallon gwamnati makarantun Islamiyya a Katsina 

A ranar Talata ne ƴan majalisan dokokin jihar Katsina suka tattauna yiwuwar maida duka wuraren kallo da gwamnati ta gina a kauyuka da garuruwan jihar zuwa makarantun Islamiyya.

Ɗan majalisan dake wakiltan karamar hukumar Jibia ne ya jagoranci muhawarar a zauren Majalisar jihar.

“Lokaci yayi da za a maida gidajen kallon Talbijin da aka giggina a kauyukan su koma makarantun Islamiyya domin sune ake bukata yanzu ba wuraren kalle-kalle ba.

“Na yi hira da wasu ƴan bindiga kuma koken da suka yi min kenan na rashin makarantu da suke fama da su. Sannan kuma su kansu wuraren kallo da yawa daga cikin su sun zama kufayi, sun lalace.

“Idan majalisa ta amince da wannan kudirin za a samu saukin Almajirai dake gararamba a jihar sannan kuma za a ɗibi malamai wanda zasu rika karantar da yara, shima hakan hanyar samar da aikin yi ne.

“Tarbiyya ya tabarbare saboda rashin ilimin addini da yayi karanci wa yara. Wannan zai sa su san addinin su sannan sukuma ilmantu.

“Wasu daga cikin gidaden kallon sun zama matattaran ƴan iska.”

A karshe kakakin majalisar Tasi’u Maigari ya mika kudirin ga kwamitin addini domin su duba sannan su baiwa majalisar shawara kan abinda ya kamata suyi.

Jihar Katsina, kamar wasu jihohin Arewa Maso Yamma, na fama da tsananin rashin tsaro.

Hare-haren ƴan bindiga yayi tsanani sace yaran makaranta.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: