Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Gwamnatin Katsina ta sa harajin N2,000 a shekara ga duk mazaunin jihar 
Gwamnatin Katsina ta sa harajin N2,000 a shekara ga duk mazaunin jihar 

Gwamnatin Katsina ta sa harajin N2,000 a shekara ga duk mazaunin jihar 

0

Gwamnatin Katsina ta sa harajin N2,000 a shekara ga duk mazaunin jihar 

..Jangalin Sanuwa 500 Duk Shekara A Matsayin Kudin Jangali

Daga Blue Ink Hausa 

Majalisar Zartaswar Jihar Katsina, karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta amince kowane mazaunin jihar Katsina, da ya kai shekara goma sha takwas da ya dunga biyan harajin naira dubu biya a duk shekara.

Kwamishinan Kasafin Jihar Katsina Da Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Jihar Katsina, Alhaji Faruq Lawal Jobe ne ya bayyana haka bayan kammala taron majalisar Zartaswar Jihar Katsina da ta saba yi duk ranar Laraba.

Alhaji Faruq Lawal Jobe ya kara da cewa wannan haraji ya shafi ma’aikacin gwamnati da wanda ba ma’aikacin gwamnati ba, ko mai Sana’a ko mai zaman banza, ko dan jihar Katsina ko ba dan jihar Katsina bane ya wajabta ka biya, Amma wajen Mata ne kawai mu ka ce sai mace mai aikin albashi, su ne kadai za su biya wannan haraji, matan da ke zaune gida ban da su, an cire su.

Jobe ya ci gaba da cewa “wannan haraji ana kiransa da harajin raya kasa. Wajen maganar yadda za’a karbi harajinza mu bullo da wani tsari da zai dauki bayanan yawan dukiya da hoto da wani katin ko na kuria ko katin zama dan Kasa da lambar BVN da kuma wadanda ke makwabtaka da wanda ya biya harajin.

Alhaji Faruq Jobe ya ce jangali kuwa duk mai shanuwa zai biya naira dari biyar a kan kowane sa ko shanuwa a duk shekara.

Kamar yadda Blueink News Hausa ta gano kuma za’a iya tunawa majalisar Zartaswar ta taba kafa wani kwamiti wanda kwamishinan Faruq Lawal Jobe ya zagaya kowacce karamar hukumar jihar Katsina, domin jin ra’ayoyin al’umma, bayan gabatar da rahotan kwamitin ne majalisar Zartaswar Jihar Katsina ta amince da shawarwarin.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: