Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA ‘Yan bindiga sun kashe mutum 19, sun kona gari a wani harin ramuwar gayya a Katsina
‘Yan bindiga sun kashe mutum 19, sun kona gari a wani harin ramuwar gayya a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutum 19, sun kona gari a wani harin ramuwar gayya a Katsina

2

‘Yan bindiga sun kashe mutum 19, sun kona gari a wani harin ramuwar gayya a Katsina 

Daga Jaridar Taskar Labarai 

Da yammacin ranar Litanin 05-07-2021 wasu gungun ‘yan bindiga suka kai hari a kauyen Tsauwa dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Sun kai harin ne da misalin karfe 05:45pm inda suka rika bin mutane kan babura suna harbewa.

Sannan kuma sun kone kauyen baki daya sai abinda ba’a rasa ba, sun sace shanu da kananan dabbobi masu yawan gaske.

A zantawar mu da mutanen kauyen sun bayyana mana cewa lokacin da abin ya faru sun sanar wa jami’an tsaro amma dai sunci karensu ba babbaka ba tare da samun wata tirjiya ba.

Bayan sun fita garin sun nufi kauyen ‘Yar Lumo inda suka kwana suna kida (DJ) suna harba bindigu sama suna murnar samun nasara da sukayi a Tsauwa.

An tabbatar da cewa sun kashe mutane goma sha tara sai kuma wasu da ba’a gansu ba. babu tabbacin suna raye ko kuma akasin haka.

Amma wani dan garin ya Kira wayar dan uwansa sai yaji tana hannun ‘yan bindigar, inda sukace masa kun kashe mana mutum biyu, mu kuma mun kashe maku linkin abinda kuka kashe mana.

Ga jerin sunayen mutum goma sha takwas da muka samu cikin wadan da barayin daji suka kashe a Tsauwa ciki hadda na’ibin limamin garin;
1.Mallam Bala (Rabe).
2.Abdulmudallib.
3.Sani Lawal (Atti).
4.Suleiman Ashiru.
5.Ashiru Lawal.
6.Mannir Sanusu.
7.Husamatu Kabir.
8.Mansir Ayyau.
9.Shafii Ayyau.
10.Alhaji Salisu.
11.Abdulaziz Iliya.
12.Umar Dan Shehu.
13.Tukur Wada.
14.Abubakar Mande.
15.Malam Bawo.
16.Abubakar Abdulmalik.
17.Iliya Abdulmummuni.
18.Tukur Haruna.

Comment(2)

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: