Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Latest Ma’aikata a Katsina sun koka kan cire tallafin gobarar ‘yan kasuwa daga albashinsu
Ma’aikata a Katsina sun koka kan cire tallafin gobarar ‘yan kasuwa daga albashinsu

Ma’aikata a Katsina sun koka kan cire tallafin gobarar ‘yan kasuwa daga albashinsu

1

Ma’aikata a Katsina sun koka kan cire tallafin gobarar ‘yan kasuwa daga albashinsu

Ma’aikatan gwamnati a jihar Katsina na cigaba da guna-guni dangane da cire kudi daga cikin albashin su da ake zargin gwamnatin ta cire ne a matsayin tallafi ga ‘yan kasuwar Central da suka samu ibtila’in gobara a watannin baya.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa wata gobara ta tashi a watan 22 ga watan Maris na 2021 a babbar kasuwar Central da ke Katsina da ta yi sanadiyyar lakume dukiyoyin milyoyin Nairori, sai dai ba a samu rasa rai ko da daya ba.

Bayan amsar rahoton tashin gobarar da gwamnan jihar ta Katsina Aminu Bello Masari ya yi daga shugaban kwamitin da ya nada domin gano musabbabin tashin gobarar, Tasi’u Dandagoro, gwamnan ya shelanta cewa bayan gudunmawar da ake samu daga ‘yan siyasa da sauran daidaikun mutane, gwamnatin jihar za ta ciri wani kaso daga cikin albashin ma’aikatan jihar a matsayin gudunmawar su ga ‘yan kasuwa.

Sai dai wasu daga cikin ma’aikatan da majiyar mu ta DCL Hausa ta zanta da su, sun ce, ba da yawunsu aka ciri wadannan kudade ba, don kuwa kamar yadda suka ce, kyauta ko sadaka sai da niyya.

Majiyar ta mu ta gano cewa an cire kudaden ne daga alabashin ma’aikatan ta la’akari da girman matakin albashi na ma’aikaci, ta yadda wasu ma’aikatan suka labarta cewa an cire musu sama da Naira dubu hudu da wadanda aka cirar musu sama da Naira dubu uku da Naira dubu daya da dai sauran yadda matakin albashin ma’aikaci ya kasance.

Wani ma’aikaci da ya nemi a sakaya sunansa ya ce “kawai dai an cire mana kudi, don babu yadda muka iya, kuma su ‘yan kasuwar ba za su taimaki ma’aikaci ba idan ya je wurinsu ba shi da kudi”, inji shi.

Haka zalika da majiyar ta mu ta tuntubi shugaban kungiyar kwadago na jihar Katsina Comr Hussaini Hamisu ‘Yanduna, ya ce yana Abuja wajen wani taro, amma idan ya kammala zamu magantu.

Comment(1)

  1. Kuma su Yan kasuwar ko ashi zasuba maaikacin gwamnati said sunyi Masa Karin kudi, Kuma idan kaje sayayye suka lura Kai maaikaci need to farashinka daban yake da na game garin mutane, said suce ai kudin banza kake samu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: