Join The Ktfest 2021 2nd Edition

Join The Upcoming Katsina Future Summit

Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Za’a kafa dokar hana bara a Katsina
Za’a kafa dokar hana bara a Katsina

Za’a kafa dokar hana bara a Katsina

0

Za’a kafa dokar hana bara a Katsina 

Kudurin dokar hana bara ya tsallake karatu na daya 

Majalissar Dokokin Jihar Katsina tayi yunkurin kafa wata doka da zata hana barace-barace akan titunan Jihar.

Wannan ya biyo bayan wani kudurin doka da jagoran majalisar kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Rimi, Hon. Abubakar Suleiman Abukur ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.

Mataimakin Kakakin majalisar, Hon Dalhatu Shehu Tafoki ne ya jagoranci zaman majalisar.

Wannan kudiri dai bai rasa nasaba da karuwar barace-barace akan titunan jihar wanda ya zamanto kamar wutar daji a fadin jihar.

Tuni dai wannan kudiri na kafa dokar hana bara a titunan jihar ya tsallake karatu na farko a zauren Majalissar a lokacin zamanta da Mataimakin Shugaban Majalissar Engineer Shehu Dalhatu Tafoki ya jagoranta.

Sanin kowa ne cewar a halinda ake ciki,titunan Jihar Katsina suna cika da masu barace-barace kala-kala musamman ma mata da kananan yara.

Mafi akasarin masu yawace-yawace na bara a titunan jihar suna yin hakan ne da sunan yan gudun hijira wanda a wasu lokutan idan aka bincika akan gane cewa ba yan gudun hijirar bane.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Join Katsina Book And Arts Festival

%d bloggers like this: