Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA An cafke shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu

An cafke shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu

0

An cafke shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu

Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa an kama Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da ke son ballewa daga kasar.

Ministan Shari’ar kasar kuma Antoni Janar Abubakar Malami ne ya tabbatar da kama Mr Kanu a wajen taron manema labarai da ya gudanar a Abuja ranar Talata.

Malami ya kara da cewa an kama shugaban IPOB ne ranar Lahadi kuma za a gurfanar da shi a gaban kuliya kan zarge-zargen da ake yi masa na neman ballewa daga Najeriya.

Kanu yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin amanar kasa lamarin da ya sa aka gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa fafutukar da yake yi wajen ganin an kafa kasar Biafra ta hanyar IPOB.

A watan Afrilun 2017 aka bayar da belinsa bisa dalilai na rashin lafiya sai dai ya tsere daga kasar.

Daga bisani ne jami’an tsaron Najeriya suka ayyana IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: