Buy High Quality Paints in Katsina Call: 08032342050

Office of the S. S. A. to Gov Masari

Visit Sahel Medicare Pharmacy & Dental Clinic Today

Visit TIS Dental & Medical Services Today

SPONSORED: JARMA 2023 FRONTERS

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

BUY TYRES/RIMS IN KATSINA 08032222751

VISIT MAIDABINO INVESTIMENT FOR ALL YOUR TASTY NEEDS

CONTACT KATSINA POST

ALBHUSTAN HOTELS LTD KATSINA

BUY ALL KINDS OF PLOTS/HOUSES/RENTS IN KATSINA

Home Katsina Post HAUSA Fallasa: Za’a gurfanar da Mahdi Shehu gaban kotu 2 gobe
Fallasa: Za’a gurfanar da Mahdi Shehu gaban kotu 2 gobe

Fallasa: Za’a gurfanar da Mahdi Shehu gaban kotu 2 gobe

1

Fallasa: Za’a gurfanar da Mahdi Shehu gaban kotu 2 gobe 

Idan za a iya tunawa an gurfanar da Mahadi Shehu a gaban Kotun tun a ranar wata Alhamis, 18/3/2021 inda ya musunta zargin da ake yi masa.

Akan haka aka dage shari’ar zuwa 19/4/2921 don soma sauraren shedu kana Alkali ya bada shi beli bisa sharadin a wuce da shi gidan yari har sai ya cika sharuddan belin.

Kafin zuwan ranar ne sai ma’aikatan Kotunan kasar nan gaba daya suka tsunduma cikin wani yajin aikin da ya kwashe sama da watanni biyu ana yi, wanda ya kawo tsaiko ga shari’ar.

Sai dai kuma a ranar Jumu’ar da aka sako Mahadi daga gidan yari na Kurmawa an ga wani faifan bidiyo na yawo wanda ya yanke hamzarin duk wani mai shakku game da lafiya ko rashin lafiyar Mahadi.

A halin da ake ciki kuma, ita ma Babbar Kotun sauraren daukaka kararraki ta Katsina ta tsaida gobe Litinin 28/6/2021 don bada bahasi akan koken da Mahadi Shehu ya shigar yana kalubalantar ingancin hanyar da Babbar Kotun Musulunci dake Katsina ta bi wajen sada shi da sammacin karar da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa ya kai shi akan zargin ya bata masa suna.

Za a saurari bahasin Alkalan uku da suka karbi koken a zaman su na Dutsinma karkashin jagorancin Maishari’a Musa Danladi Abubakar da karfe 9:00am a zauren Kotu ta 3 dake harabar kotu ta Jihar Katsina dake kan hanyar Daura.

Comment(1)

  1. Wane irin incomplete labari ne haka. Ya kamata daga karanta wa mu san wane shi Mahadi? Me ya kai shi kotun ? Ba wai sai kana bin labarin shine zaka gane ba.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: