
Za mu dauki masu gadi 1,000 aiki don tsare makarantun kwanan jihar Katsina – Masari
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce ya bayar da umurnin daukar ma’aikatan gadi mutum dubu daya domin tura su zuwa makarantun Sakandare na kwana a duk fadin jihar Katsina domin kara samar da cikakken tsaro ga daliban.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau a yayin jawabin sa wajen bikin yaye dalibai karo na uku na Jami’ar Umar Musa Yar’adua dake Katsina a yau Asabar.
Masari ya ce daukar masu gadin na cikin shirin tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.
” Duk da dai a yanzun jihar Katsina na cikin jihohi masu tsaro da zaman lafiya, amma duk da haka ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen ba daliban jihar mu kyakkyawan tsaro ” inji Masari.
Gwamnan ya bayyana cewa tun da aka rantsar da shi a matsayin Gwamnan jihar Katsina a 2015 zuwa yanzun babu abin da gwamnatinsa ta fi fifitawa kamar dabbaka darajar Ilimi.
Ya ce ko a farkon watan Janairu 2018 zuwa yanzun sun bada aikin gyaran makarantar Government Technical College Mashi a kan kudi naira miliyan N277 .
Ya kara da cewa an kuma bada gyaran makarantar Government Day Secondary School, Yanduna dake cikin karamar hukumar Baure a kan naira miliyan N27.5.
” Haka kuma mun bada aikin gyaran makarantar Government Girls Boarding Secondary School, Rogogo dake a karamar hukumar Zango a kan kudi naira miliyan N263.1 , sannan mun bada aikin gyaran makarantar Government Girls Secondary School, Sandamu a kan kudi naira miliyan N278.8.
” Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da kudi naira miliyan N90.1 domin gyaran makarantar Government Day Secondary School, Tama a karamar hukumar Bindawa . Inji Masari .
Haka kuma Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta aminta da daukar sabbin malaman koyarwa da wadanda ba na koyarwa ba a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina da kuma Kwalejin Ilimi ta Isa Kaita dake Dutsin-ma .
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya rawaito cewa dalibai 1,397 ne Jami’ar ta yaye a yau daga cikinsu 1,290 ne suka kammala Digirin farko sai kuma 107 suka kammala karatun babban Digiri na biyu a Jami’ar.