Access professional Dental and Pharmaceutical Services in Katsina Call: 08100881729

CONTACT KATSINA POST

Buy Mobile Phones Contact 08035947436

Visit Sahal Pharmacy & Stores Today!

Buy New or Exchange Tyres & Rims in Katsina Call: 08032222751

CLICK TO REGISTER NOW!!!

MAIDABINO INVESTMENT LTD.

Home Katsina Post HAUSA Ku sadu da AIG M. M. Katsina – Dan sandan da ka iya maye gurbin Ibrahim Idris
Ku sadu da AIG M. M. Katsina – Dan sandan da ka iya maye gurbin Ibrahim Idris

Ku sadu da AIG M. M. Katsina – Dan sandan da ka iya maye gurbin Ibrahim Idris

0

By Gidado S.

Da zaran akayi wani zama kan canza fasalin shugabanci na Rundunar Yan’sandar Nigeria (NPF), Shugaban Yan’sanda Najeriya na kasa IGP Ibrahim Kpotum Idris na iya rasa kujerar sa.

Dalili kuwa shine, ana kyautata zaton shugaba Muhammadu Buhari ya bada ummurnin tantamce manyan Yan’sandan domin maye gurbin IG Ibrahim Idris, a cewar kafar yada labarai ta Nigerian Independent.

Rahoton wanda Nigerian Independent ta watsa yace, shugaba Muhammadu Buhari ya damu akan zarge-zargen Cin hanci da ake yima IGP din da kuma zargin nuna 6angarenci wajen gudanar da aikin da dora masa.

Ko kwanannan sai da yayi, ‘kunanan uwar shegu’ da ummurnin da shugaba Buhari ya bashi na, ya baro helkwatar yan’sandan dake Abuja ya tare a Benuwai, wannan ma na daya daga cikin dalilan safke IGP din.

An bada rahotan cewa, mataimaka 2 masu mukamin  DIG (Deputy Inspector of Police) da kuma wasu 3 masu mukamin AIG (Assistant Inspector of Police), ana tantamce su domin za6ar wanda a ba ragamar tafiyar da shugabanci rundunar yan’sandan. Wadanda ake tantamcewar sun hada, DIG Shu’aibu Gambo, mai kula rukunin ‘A’ na 6angaren sha’anin tafiyar hukumar (watau Admin Department) ya fito ne daga jihar Niger DIG Habila Joshak, mai kula da rukunin ‘B’ (Operation Department ), AIG Muhammad Musa Katsina, mai kula da Sintirin Bakin iyakar kasa (Border Patrol), ya fito ne daga jaha daya shida shugaba Buhari, AIG Adamu Mohammed Abubakar mai kula da Zone 5 na Rundunar Yan’sandan, ya fito ne daga jahar Nasarawa sai kuma AIG Kayode Aderanti, ya fito daga jahar Osun.

Ana kyautata tsammani daga cikin wadannan manyan yan’sanda da ake zaton an tantamce guda 5, AIG Mohammed Musa Katsina ya zarce su wajen nuna kwazo da kuma cimma nasarorin rundunar ta yan’sandan.

Daga cikin kwazo da nasarori da Mohammed M. Katsina yayi sun hada da; ya jagoranci ‘National Institute for Policy & Strategic Studies, Kuru wanda ke kusa da Jos, an kara mashi daga Kwamishinan Yan’sanda zuwa AIG a 2016.

AIG M. M. Katsina shine wanda fadar sunan sa kawai yake tayar hankalin duk wani mai aikata lefi a Nigeria.

Daga cikin kokarin da yayi na nasara kan masu aikata lefuffuka sun hada da, cafke 6arayin shanu, masu satar mota, gano da kama masu harkar sayar jarirai da kuma cafke yan-ina-da kisa masu cin karen su ba babbaka, wayan’da suke ma al’ummah fashi, da dai sauransu.

LEAVE YOUR COMMENT

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: